Nigeria TV Info
NDLEA Ta Yi Samame a Wani Kulob Din Dare a Lagos, Ta Kama Pretty Mike, Tsohon Dan BBN Tuoyo, da Sama da Mutane 100
Hukumar yaki da fataucin miyagun
Æwayoyi ta Æasa, NDLEA (National Drug Law Enforcement Agency), ta gudanar da samame a wani sanannen kulob din dare da ke birnin Lagos, inda ta kama shahararren Éan kasuwa Pretty Mike, tsohon Éan gidan Big Brother Naija, Tuoyo, tare da fiye da mutane 100.
Shaidu sun ce jamiâan NDLEA sun isa wurin da misalin karfe 2 na dare, suka rufe dukkan Æofofi, sannan suka fara gwajin miyagun Æwayoyi ga mutanen da ke wurin. An gano wasu Æwayoyi kamar ecstasy, cannabis, da molly a cikin wurin.
Mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa wannan aiki wani Éangare ne na yunkurin hukumar wajen dakile yaduwar miyagun Æwayoyi a wuraren nishadi da otal-otal a fadin Æasar. Ya Æara da cewa hukumar za ta ci gaba da wannan aiki domin tabbatar da tsafta a fagen nishaÉi da yawon shakatawa.
Sharhi