TRUMP YA YI GARGADI GA SABON SHUGABAN VENEZUELA: “ZA TA BIYA FARASHI MAI TSANANI”
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar cewa sabuwar shugabar rikon-kwarya ta Venezuela, Delcy Rodríguez, za ta fuskanci “babban farashi — ma fiye da na Maduro” idan ta ki yin aiki tare da Amurka bayan kifar da tsohon shugaban Nicolás Maduro.
Trump ya ce Washington na sa ran Caracas ta bude damar zuba jari a fannin man fetur, ta kuma karfafa yaki da safarar miyagun kwayoyi. Rodríguez ta bayyana cewa har yanzu Maduro ne halal na kasa, tana kuma zargin Amurka da karya doka da tsoma baki cikin harkokin cikin gida.
Masu nazari sun ce gargadin na iya kara tayar da hankali tsakanin kasashen biyu, yayin da wasu kasashen Latin Amurka da jami’an Majalisar Dinkin Duniya ke sukar matakin soji na Amurka da kama Maduro. A halin yanzu, zanga-zanga da kiraye-kiryen diflomasiyya na kara karfafa a Venezuela.
Sharhi