Nigeria TV Info
Shekarau Ya Kare Shirin Sauya Sheka Na Gwamna Yusuf Zuwa APC, Ya Tuna Da Abin Da Kwankwaso Ya Taba Yi
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, ya kare matakin da ake cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin Éauka na komawa jamâiyyar APC daga NNPP. Shekarau ya ce sauya sheka ba cin amanar kowa ba ne, domin siyasa tana tafiya ne da yanayi da shawarar manyan masu ruwa da tsaki.
A cikin wata magana da ta yadu a kafafen sada zumunta, Shekarau ya soki sukar da Rabiu Musa Kwankwaso ya yi, inda ya tuna cewa Kwankwaso ma ya taba barin PDP ya koma APC a da, ba tare da ya miÆa mulki ba. Ya ce bai dace a zargi wani da abin da ka taÉa aikatawa ba.
Shekarau ya kuma tabo batun matsalolin cikin gida da suka taso a lokacin kafa NNPP, musamman kan rabon mukamai, wanda ya haifar da rarrabuwar kawuna. Ya bayyana cewa kowane shugaba yana da âyancin tantance inda siyasar sa ta fi masa amfani bayan shawara da jamaâa.
Yayin da ake cigaba da tattaunawa kan lamarin, rahotanni na nuna APC na ÆoÆarin karÉar Gwamna Yusuf, lamarin da ke Æara Æuna a siyasar Kano, musamman ganin yadda zaben 2027 ke Æara matsowa.
Sharhi