Nigeria TV Info â UNICEF Ta Bayar da Gargadi Kan Rashin Samun Kayan Gina Jiki Ga Kashi 60% Na Mata Masu Juna Biyu a Najeriya
Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya nuna damuwa kan lafiyar mata masu juna biyu a Najeriya, inda ya bayyana cewa kusan kashi 60 cikin 100 na su ba su da damar samun kayan gina jiki na micronutrient da za su kare rayukansu da na jariran da suke Éauke da su.
A cikin rahoton ci gaban yaÆin neman inganta abinci, Maâaikatar Lafiya da Walwalar Jamaâa ta Tarayya ta bayyana cewa kashi 58 cikin 100 na mata masu haihuwa a Najeriya suna fama da cutar anaemia â wadda ake alaÆanta da rashin wadataccen abinci mai gina jiki.
A cewar jamiâin abinci na UNICEF, Prosper Dakurah, Najeriya na matsayi na farko a Afirka kuma ta biyu a duniya wajen yawan masu fama da rashin abinci mai gina jiki.
Dakurah ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja yayin taron manema labarai kan âHana da Rage Anaemia da Sauran Matsalolin Abinci Mai Gina Jiki a Najeriya,â wanda Kungiyar Civil Society Scaling Up Nutrition in Nigeria (CS-SUN) ta shirya. Ya ce matsalar ba ta tsaya ga Æarancin Æarfe (iron) kaÉai ba, har da sauran muhimman sinadarai na micronutrients.
Ya Æara da cewa gwamnati tare da haÉin gwiwar abokan cigaba sun fara samar da kayan koyarwa domin Æarfafa maâaikatan lafiya su rarraba kayan gina jiki na micronutrient ga mata masu juna biyu a fadin Æasar.
UNICEF ta jaddada cewa akwai buÆatar Éaukar mataki cikin gaggawa wajen magance matsalar rashin abinci mai gina jiki a tsakanin mata masu juna biyu domin kare lafiyar uwa da tabbatar da haihuwa cikin aminci.
Sharhi