Nigeria TV Info â Rahoton Labarai
A wani babban ci gaba wajen dakile yaduwar cutar HIV a duniya, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta amince da amfani da lenacapavir (LEN) na allura a matsayin sabon zaÉin rigakafin HIV kafin kamuwa da ita (PrEP).
An sanar da wannan sabuwar shawarar yayin taron Æungiyar AIDS ta duniya karo na 13 (IAS 2025) da aka gudanar a Kigali, Rwanda â wanda ke nuna wani muhimmin juyi a yaÆin da ake yi da cutar HIV.
A cewar WHO, lenacapavir â wanda ake yi wa mutum allura duk bayan watanni shida â ya nuna Æarfin Æwarai wajen hana kamuwa da cutar ga waÉanda ke cikin haÉarin kamuwa da HIV. Ana sa ran cewa wannan tsari na dogon lokaci zai taimaka wajen Æara bin kaâida fiye da magungunan kwayoyi na baki da ake sha kullum, wanda ya kasance Æalubale a alâummomi da dama.
Masana harkar kiwon lafiya sun yaba da wannan mataki, suna mai jaddada cewa yin allura sau biyu a shekara na iya taimakawa wajen cike gibi a bangaren rigakafin HIV, musamman a Æasashe masu Æaramin ko matsakaicin Æarfin tattalin arziki. Haka kuma, WHO ta bukaci kasashen duniya da su sabunta shirye-shiryen rigakafin HIV na Æasashensu domin haÉa LEN tare da tabbatar da cewa kowa zai iya samun damar amfani da shi.
Yayin bayani a taron, Darakta Janar na WHO, Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana wannan shawarar a matsayin âmuhimmin juyiâ tare da kira ga gwamnatoci da abokan aikin kiwon lafiya da su gaggauta daukar matakai don samar da wannan sabuwar hanya ga jama'a.
Shigowar LEN wani bangare ne na kokarin da ake yi na kawo Æarshen cutar AIDS a matsayin barazanar lafiyar jamaâa nan da shekarar 2030. Hukumar lafiya ta duniya da sauran hukumomi sun ce haÉa sabbin fasahohi kamar lenacapavir da kuma ci gaba da samun damar gwaji da magani na da matuÆar muhimmanci wajen cimma wannan manufa.
Sharhi