Nigeria TV Info Rahoto
Lauyan kare hakkin dan Adam, Femi Falana (SAN), ya bukaci gwamnati tarayya da jihohi su shimfiÉa kyautattun hidimomin lafiya ga matan da ke juna biyu marasa Æarfi a faÉin Æasar, yana mai jaddada cewa wannan shi ne hanya mafi inganci wajen rage mace-macen mata masu juna biyu da jarirai a Najeriya.
Falana, wanda ya yi wannan kira cikin wata sanarwa a ranar Lahadi a matsayinsa na Shugaban Alliance on Surviving COVID-19 and Beyond (ASCAB), ya ambaci wasu shirye-shiryen da hukumomin lafiya suka Æaddamar domin rage mace-macen mata masu haihuwa.
Ya tuna cewa a watan Nuwamba bara, Ministan Lafiya da Walwalar Jamaâa, Far. Muhammad Pate, ya bayyana cewa za a rika yi wa mata âyan Najeriya da suka bukata aikin haihuwa ta tiyata (caesarean section) kyauta, ÆarÆashin shirin âMaternal Mortality Reduction Innovation Initiative.â
Haka kuma Falana ya ce a watan Afrilu bana, Hukumar Inshorar Lafiya ta Æasa (NHIA) ta tabbatar da cewa ta fara bayar da aikin haihuwa ta tiyata kyauta ga matan da ke juna biyu a asibitoci fiye da 100 a faÉin Æasar.
A cewarsa, Shugaban NHIA, Dakta Kelechi Ohiri, ya bayyana cewa wannan shirin ana aiwatar da shi ÆarÆashin Comprehensive Emergency Obstetric and Neonatal Care Programme.
Duk da yake ya yaba da waÉannan matakai a matsayin hujjar jajircewar gwamnati wajen yakar mace-macen mata masu haihuwa da jarirai, Falana ya jaddada cewa wajibi ne a faÉaÉa shi fiye da yadda yake yanzu don ya haÉa dukkan matan da ke juna biyu marasa Æarfi a Najeriya.
Sharhi