An shiga cikin firgici a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, bayan wasu fashe-fashe da suka auku a sassa daban-daban na birnin, lamarin da ya haifar da fargabar mutuwar mutane da jikkatawa.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa sun ji karar fashewar bam sau da dama cikin kankanin lokaci, lamarin da ya haddasa ruÉani a yankunan da ke kusa. Har yanzu ba a tabbatar da ainihin wuraren da lamarin ya shafa ba.
Rahotanni daga majiyoyi na cikin gida sun ce jamiâan agaji da na tsaro sun isa wuraren da abin ya faru, yayin da asibitoci ke karÉar waÉanda suka jikkata. Har yanzu ba a san adadin mutanen da abin ya shafa ba.
Hukumomi ba su fitar da cikakken bayani ba zuwa yanzu, amma an daÉe ana fama da irin waÉannan hare-hare a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
An shawarci mazauna yankin da su zauna cikin gida tare da yin taka-tsantsan yayin da jamiâan tsaro ke ci gaba da bincike.
Sharhi