Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.8 Ta Girgiza Kudancin Philippines, Ta Haddasa Fargabar Tsunami

Rukuni: Tarihi |
Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.8 Ta Girgiza Kudancin Philippines, Ta Haddasa Fargabar Tsunami
Wata babbar girgizar kasa mai karfin maki 7.8 ta afku a kudancin ƙasar Philippines, lamarin da ya haifar da fargabar tsunami tare da jefa mazauna yankunan da abin ya shafa cikin tashin hankali.
Rahotanni sun bayyana cewa girgizar kasar ta yi barna ga gine-gine da kayayyakin more rayuwa, yayin da jami’an agaji da ceto ke ci gaba da gudanar da ayyukan ceton wadanda abin ya shafa. Hukumomi sun bukaci mazauna yankunan bakin teku da su koma wurare masu tudu domin kariya daga yiwuwar tasirin tsunami.
Gwamnatin Philippines ta fara daukar matakan gaggawa tare da tura jami’an ceto, kayan agaji da sauran kayan tallafi zuwa yankunan da abin ya shafa. Masana sun kuma gargadi jama’a da su kasance cikin shiri saboda yiwuwar sake aukuwar girgizar kasa (aftershocks).

Sharhi

Ka kasance da mutunci. Babu maganganun kiyayya ko spam.

Babu sharhi tukuna.