Nigeria TV Info.
Rundunar Sojan Ruwa ta Pakistan za ta kaddamar da jirgin karkashin ruwa na farko da kasar Sin ta kera, wanda ake kira Hangor-class submarine, a shekara mai zuwa. Wannan mataki na nuna karuwar hadin gwiwar soja tsakanin Islamabad da Beijing, tare da kara tsananta takaddama ta dabarun tsaro da Indiya.
Shugaban Rundunar Sojan Ruwa ta Pakistan, Admiral Naveed Ashraf, ya tabbatar wa jaridar Global Times ta kasar Sin cewa shirin jirgin karkashin ruwa — wanda ya kunshi jirage guda takwas, a karkashin yarjejeniyar dala biliyan 5 — yana tafiya cikin nasara.
Karkashin yarjejeniyar, jiragen ruwa guda hudu za a kera su a kasar Sin, yayin da sauran hudu za a kera su a Pakistan, domin karfafa kwarewar masana'antar jiragen ruwa na cikin gida.
Pakistan ta riga ta kaddamar da jiragen ruwa guda uku daga masana’antar jiragen ruwa ta kogin Yangtze da ke lardin Hubei, kasar Sin.
Admiral Ashraf ya yaba da fasahar da ingancin kayan yaki na kasar Sin, yana mai cewa suna biyan bukatun aikin rundunar. Ya kuma bayyana cewa rundunar tana fadada ayyukanta zuwa fannin Artificial Intelligence (AI), jiragen marasa matuki da yaki ta hanyar lantarki tare da kasar Sin a matsayin babban abokin hadin gwiwa.
Sabbin jiragen ruwa na Hangor-class za su kara karfin Pakistan wajen gadin teku a yankin Arewa maso Yammacin Tekun Arabiya da kuma tekun Indiya gaba daya.
Sharhi