Nigeria TV Info
2027: ‘Yan sanda da INEC sun yi gargaɗi kan kamfe tun da wuri
Rundunar ‘Yan sandan Najeriya tare da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) sun gargadi jam’iyyun siyasa da magoya bayansu da su guji fara yaɗa kamfen kafin lokacin da doka ta tanada.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce hukumar ba ta fitar da jadawalin zaɓe ba tukuna. “Doka ta bayyana. Duk wani kamfe ko tallar siyasa kafin lokacin da aka kayyade ya sabawa dokar zaɓe, kuma za a hukunta masu karya wannan doka,” in ji shi.
Kakakin ‘Yan sanda na ƙasa, ACP Muyiwa Adejobi, ya ce jami’an tsaro za su aiwatar da doka ba tare da nuna son kai ba. “Mun lura da fara ɗora poster da gudanar da tarukan siyasa a wasu wurare. Wannan laifi ne, kuma duk wanda aka kama za a gurfanar da shi a kotu,” in ji shi.
Duka hukumomin sun bukaci shugabannin jam’iyyun siyasa da su horar da magoya bayansu wajen bin doka da kuma mayar da hankali wajen inganta dimokuraɗiyya.
Masu nazari sun ce wannan gargadi ya zo ne a daidai lokacin da jam’iyyu ke fara shirye-shiryen fafatawa a zaɓen 2027.
Sharhi