Nigeria TV Info – Labaran Duniya
Sarkin Qatar Ya La’anci Kisa da Cin Zarafin Mutane a Al-Fashir, Ya Nemi Gaggawar Dakatar da Rikici
Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, ya bayyana rashin jin daɗinsa tare da la’antar abin da ake zargin an aikata wa fararen hula a birnin Al-Fashir na Sudan, yayin da rikici ke ƙaruwa tsakanin sojojin Sudan da dakarun Rapid Support Forces (RSF).
Yayin jawabi a birnin Doha ranar Talata a lokacin bude taron Second World Summit for Social Development, Sarkin ya nuna damuwa matuka dangane da halin da ake ciki a lardin Darfur ta Arewa.
“Ba zan rufe wannan jawabi ba tare da nuna mamakinmu da alhini game da mummunan abin da aka aikata a birnin Al-Fashir a Sudan, da kuma la’anar da muke yi masa,” in ji shi.
An ruwaito cewa Al-Fashir ta fada karkashin ikon RSF bayan makonni 18 na kewaye wanda ya hana abinci, magunguna da kayan agaji shiga. Kungiyoyin agaji da majiyoyi na cikin gida sun bayar da rahoton cin zarafin bil’adama da suka hada da kisan gilla, fyade, kashe ma’aikatan agaji, korar jama’a da sace-sace.
Sharhi