Dakarun Isra’ila Sun Kashe Iyalan Falasdinawa Hudu A Harin Bindiga A West Bank
Dakarun Isra’ila sun harbe tare da kashe wani ma’aurata Falasdinawa da ‘ya’yansu biyu kanana a wani lamari da ya faru a yankin West Bank da Isra’ila ke iko da shi, kamar yadda hukumomin Falasdinawa suka bayyana.
Iyalan da aka kashe sun hada da Ali Bani Odeh da matarsa Waad Bani Odeh. Rahotanni sun ce iyalan na cikin mota tare da ‘ya’yansu lokacin da dakarun Isra’ila suka bude musu wuta a garin Tammum da ke arewacin West Bank.
Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu ta ce daga cikin wadanda aka kashe akwai Mohammed mai shekaru biyar da Othman mai shekaru bakwai.
Jami’an lafiya sun bayyana cewa an kai gawarwakin mutane hudu asibiti da raunukan harsashi a kai da fuska.
Wasu yara biyu da ke cikin motar a lokacin harin — masu shekaru takwas da goma sha daya — sun tsira, amma sun samu kananan raunuka sakamakon gutsuttsuran harsashi.
Harin ya kara dagula yanayin tsaro a yankin West Bank inda tashin hankali tsakanin dakarun Isra’ila da Falasdinawa ke karuwa a ‘yan watannin nan.
Hukumomin Falasdinu sun yi Allah-wadai da harin tare da kira ga a gudanar da binciken kasa da kasa kan lamarin.
Sharhi