Nigeria TV Info
Google za ta zuba Dala biliyan $15 a India, ta gina cibiyar AI mafi girma a wajen Amurka
Kamfanin fasaha na duniya Google ya bayyana cewa zai zuba dala biliyan $15 cikin shekaru biyar domin gina babbar cibiyar Artificial Intelligence (AI) da Data Centre a birnin Visakhapatnam, Andhra Pradesh, kasar India. Wannan zai zama cibiyar AI mafi girma da Google za ta gina a wajen Amurka.
Rahoton Reuters ya ce cibiyar za ta kasance da tsarin makamashi mai tsafta (clean energy), fibre-optic network, da kuma tashar kebul na karkashin teku (subsea cable landing station) da za ta haÉa India da sauran yankunan duniya.
Shugaban Google Cloud, Thomas Kurian, ya bayyana cewa wannan zuba jari na da muhimmanci don biyan bukatar da ke Æaruwa a fannin AI. Gwamnatin tarayya da ta jihohi a India sun bayyana goyon baya ga shirin, suna mai cewa zai taimaka wajen sa India ta zama cibiyar fasahar AI mafi tasiri a duniya.
Hakan na zuwa ne yayin da Microsoft, Amazon, da wasu kamfanonin AI masu tasowa ke kuma Æara zuba jari a India, abin da ke kara Æarfafa matsayin Æasar a fagen fasahar zamani da AI.
Sharhi