Nigeria TV Info
Zargin Ta’addanci: Ban Da Laifi Ba, Ku Sake Ni — Nnamdi Kanu Ya Faɗa Wa Kotu
Shugaban ƙungiyar IPOB da aka haramta, Nnamdi Kanu, ya roƙi Babbar Kotun Tarayya dake Abuja da ta watsar da shari’ar ta’addanci da gwamnatin tarayya ke masa, yana mai cewa babu hujjar da ke nuna yana da hannu a wani laifi.
Lauyan Kanu ya shaida wa kotu cewa gwamnati ta kasa gabatar da wata shaidar da ke tabbatar da zargin ta’addanci ko wani aiki na ɓata gari. Ya kuma ce tsare Kanu tun bayan kamo shi a shekarar 2021 ya sabawa ‘yancin ɗan adam.
Sai dai lauyan gwamnatin tarayya ya roƙi kotun da ta ci gaba da shari’ar, yana mai cewa akwai hujjoji da za su tabbatar da laifin Kanu. Mai shari’a Binta Nyako ta dage zaman don yanke hukunci kan roƙon Kanu na “babu hujja” wato “no-case submission.”
Shari’ar ta jawo hankalin ƙasashen duniya da kungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam, waɗanda ke kira ga gwamnati da ta tabbatar da adalci da gaskiya a cikin shari’ar.
Sharhi