Zaben Anambra: Amupitan Ya Fuskanci Gwajin Gaskiya Yayin Da Mutane Miliyan 2.8 Ke Kada Kuriâa A Yau
Fiye da mutane miliyan 2.8 ne za su fita kada kuriâa yau a zaben gwamnan Jihar Anambra domin tantance wanda zai ja ragamar mulki na shekaru hudu masu zuwa. Wannan shi ne zabe na farko da ake gudanarwa tun bayan hawa sabon shugaban hukumar zabe ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, wanda ya kama aiki a ranar 23 ga Oktoba.
Masu lura da shaâanin siyasa sun bayyana cewa wannan zabe ne zai nuna sahihancin INEC wajen gudanar da sahihin zabe mai inganci da gaskiya.
Babban Gwamna mai ci, Farfesa Chukwuma Soludo na jamâiyyar APGA, na neman waâadi na biyu, yayin da manyan âyan takara suka hada da Prince Nicholas Ukachukwu (APC), Dr. George Moghalu (LP), Jude Ezenwafor (PDP), John Nwosu (ADC), da Sir Paul Chukwuma (YPP).
INEC ta tabbatar da cewa an shirya komai â akwai rukunin zabe 5,718, naâurorin BVAS 6,879, da maâaikatan wucin gadi sama da 24,000. An rarraba kayan zabe zuwa kananan hukumomi tun ranar Alhamis a karkashin tsaro mai tsauri.
Rundunar âyan sanda ta jihar ta sanar da takaita zirga-zirgar ababen hawa daga karfe 12 na dare zuwa 6 na yamma domin hana matsalolin tsaro. Akalla jamiâan tsaro 55,000 ne aka tura don kare masu kada kuriâa da maâaikatan INEC.
Kungiyoyin lura da zabe irin su Yiaga Africa, CDD, da CTA sun kafa cibiyoyin sa ido a jihar, yayin da INEC ta tura kwamishinoni na kasa da na jihohi don sa ido kan zaben. Hukumar ta tabbatar da cewa zabe zai gudana cikin lumana duk da matsalolin tsaro a Ihiala da wasu yankuna.
Sharhi