Shugaban Amurka Donald Trump Ya Bai wa Ukraine Ƙaramin Wa’adin Amincewa da Tsarin Zaman Lafiyan da Aka Ce Yana Wa Russia Rinjiya
A wani mataki da ya tayar da ce-ce-ku-ce a duniya, Shugaban Amurka Donald Trump ya bai wa Ukraine kasa da mako guda ta amince da tsarin zaman lafiya mai matakai 28 — wanda ake suka sosai saboda ana ganin yana fifita Russia — domin kawo ƙarshen yakin da ya kai kusan shekaru huɗu.
Rahotanni sun ce shirin yana buƙatar manyan sauye-sauye daga Kyiv, ciki har da mika wasu yankunan Donbas, rage karfin rundunar sojinta, da daina burin shiga NATO.
Trump ya sa ranar Thanksgiving (alhamis mai zuwa a Amurka) a matsayin wa’adi da ya dace Ukraine ta rattaba hannu. Ya kuma barazana da dakatar da musayar bayanan leken asiri da tallafin makamai idan Ukraine ta ƙi.
A cikin jawabin kasa, Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya ce kasarsa na fuskantar “ɗaya daga cikin mawuyatan lokuta” a tarihin ta. Ya gargadi cewa amincewa da shirin Trump na iya nufin rasa mutunci, ‘yanci da adalci.
Zelenskyy ya ce bai yarda da tattaunawar da za ta haɗa da “musayar yankuna” da Russia ba, yana mai cewa Ukraine “ba za ta ba wa Russia wata kyauta kan abin da ta aikata ba.” Duk da haka, ofishinsa ya tabbatar cewa sun karɓi takardar shirin kuma a shirye suke su shiga tattaunawa ta diflomasiyya.
Shugabannin Turai sun nuna damuwa, suna cewa duk wata yarjejeniyar zaman lafiya dole ta mutunta cikakken ikon Ukraine kuma ba ta zama mika wuya ba.
Sharhi