Tattalin arziki Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da cewa ta tara kusan ₦600 biliyan daga harajin VAT da ake karɓa daga manyan kamfanonin intanet na ƙasashen waje irin su Facebook, Google, Netflix da sauransu.