Nigeria TV Info
CBN Ta Bayyana Mataki Na Gaba Ga Bankunan Najeriya Biyar Da Suka Gaza Cika Ka’idar Karin Jari
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa bankuna biyar da har yanzu ba su cika sabbin ka’idojin karin jarin bankuna ba za su ci gaba da gudanar da harkokinsu yayin da ake kokarin warware matsalolin doka da na tsarin gudanarwa da suka hana su kammala shirin.
Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya bayyana hakan bayan taron Kwamitin Manufofin Kudi (MPC), inda ya ce bankunan ba su cikin matsalar rugujewa, sai dai suna fuskantar jinkiri wajen kammala matakan tara karin jari.
A cewarsa, bankuna 33 sun riga sun cika sabon sharadin karin jari da CBN ta gindaya domin karfafa tsarin bankunan Najeriya da tabbatar da dorewar bangaren hada-hadar kudi.
Cardoso ya kara da cewa wasu daga cikin bankunan da abin ya shafa sun taba fuskantar matakan hukunci daga masu kula da harkokin banki, lamarin da ya rage musu lokacin da za su kammala shirin karin jarin.
CBN ta kuma tabbatar wa masu ajiya da masu zuba jari cewa tsarin bankunan Najeriya yana nan cikin kwanciyar hankali da tsaro, tare da kira ga jama’a da kada su firgita kan rahotannin da ke yawo game da bankunan.
Sharhi