NIGERIA TV INFO — WASAN KWALLON KAFIYA / LABARAN KWALLON DUNIYA
Ana Iya Gabatar da Sabbin Dokokin Lissafin Lokaci Don Hanzarta Wasannin Gasar Cin Kofin Duniya
Ana iya ganin wasanni masu sauri a Gasar Cin Kofin Duniya ta FIFA ta 2026 yayin da hukumar tsara dokokin kwallon kafa ke la'akari da gabatar da ƙidaya na lokaci ga saka kwallo a gefe (throw-ins), bugun ƙofa (goal kicks), da sauya ‘yan wasa.
Hukumar Kula da Dokokin Kwallon Kafa ta Duniya (IFAB), wacce ke kula da dokokin wasan, na binciken matakan sabbin dokoki bayan samun kyakkyawan ra’ayi kan ƙayyadadden lokaci na sakan takwas ga masu rike da kwallo. Bisa sabbin dokokin da ake shirin gabatarwa, alkalai za su iya amfani da ƙidayar sakan biyar a lokutan da ake tsayawa kamar throw-ins da goal kicks idan ‘yan wasa suna jan lokaci.
Haka zalika, sauya ‘yan wasa na cikin duba. ‘Yan wasa da ke shiga filin za su iya fuskantar iyaka na sakan 10 don kammala aikin. Idan aka wuce wannan lokaci, za a iya hana su shiga na ɗan lokaci, har zuwa minti ɗaya. Haka kuma, ‘yan wasa da suka ji rauni za a iya bukatar su kasance a wajen filin na wani lokaci don hana kungiyoyi yin amfani da tsayawar wasan.
Jami’an IFAB sun ce manufar waɗannan canje-canje ita ce tabbatar da gudu da saurin wasan, domin masoya su ji daɗin kallo ba tare da tsayawa ba.
Sharhi